Hukumar hana cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa watau EFCC ta bankado gidajen Akanta Janar na tarayya, Ahmad Idrs, guda goma sha bakwai (17).

Wani jami’in EFCC wanda ya buƙaci a sakaye sunansa yace Idris ya mallaki gidaje a Kano, Lagos, Abuja, Dubai da London.

Ya kara da cewa an gani Ahmad Idris ya yi amfani da wasu makusantansa wajen sayen waɗannan dukiyoyi.

Jami’n yace ga dukkan alamu, ya mallakai waɗannan dukiyoyin ne yayinda yake Ofis amma bai ayyana cikin takardar hukumar ladabtar da ma’aikata ba kamar yadda doka ta tanada.

A cewar jami’in:

“Kimanin gidaje 17 a Kano, Lagos, Abuja, Dubai da London aka bankaɗo mallakinsa.

A Abuja, an samu gidajen a wasu manyan  rukunin gidaje daje Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: