Jami’an hukumar yaƙi da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati, EFCC, a ranar Laraba sun yi ram da tsohon manajan daraktan hukumar cigaban Neja Delta, NDDC, Nsima Ekere.

An kama Nsima Ekere, bisa zargin karkatar da wasu maƙudan biliyoyi.

Ana zargin tsohon shugaban hukumar NDDC ɗin da waskar da maƙudan kuɗaɗe da suka kai N47 biliyan ta hanyar amfani da ƴan kwangila masu rijista na hukumar.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwajaren, ya tabbatar wa Channels TV hakan.

Tsohon shugaban hukumar shi ne tsohon ɗan takarar gwamnan Jhar Akwa Ibom a jam’iyyar APC a zaɓen 2019.

Nsima mai shekara 56 ya riƙe hukumar Neja Delta daga 2016 zuwa 2018.

Leave a Reply

%d bloggers like this: