Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El’rufa’i ya tabbatar da ɓullar sabuwar ƙungiya mai iƙirarin jihadi a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne yau a Kaduna yayin zman majalisar zartarwa ta jihar bayan karɓar bayani daga kwamishinan al’amuran tsaron cikin gida a Kaduna.
Gwamna El’rufa’i ya ce ƙungiyar mai suna Ansaru da mayaƙan Boko Haram na ci gaba da yaɗuwa tare da ƙaddamar da hare-hare a jihar.

Ya ce mayaƙan ƙumgiyar Ansaru ne su ka yi garkuwa da matafiya a jirgin ƙasa da ya tas daga Abuja zuwa Kaduna wanda har yanzu mafi yawa daga cikinsu ke hannun mayaƙan.

Ya ƙara da cewa mayaƙan na guduwa daga arewa maso gabashin Najeriya zuwa arewa maso yammacin jihohi.
Sannan mayaƙan na shigar da matasa cikin ƙungiyar tare da basu horo a kan hare-hare zuwa wurare daban-daban.
Idan ba a manta ba a ranar 28 ga watan Maris wasu mahara su ka kai hari kan jirgin ƙasa da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja tare da yin garkuwa da wasu.