Wasu matasa uku sun nutse a cikin ruwan Ƙaraye a lokacin da suka je wanka a koge.

wanda su ka rasu sun haɗa da Musa Abubakar mai shekara 25 da Isyaku Bashir, mai shekara 23 da kuma Nazifi Ibrahim mai shekara 19, duk sun rasu a lokacin da suka shiga dam don su yi wanka da misalin ƙarfe 11:00 na safe.

Ɗaya daga cikin abokin matasan mai suna Idris, wanda lamarin ya faru akan idonsa ya shaidawa manema labarai yadda lamarin ya faru:

Idris ya fara da cewa shi da sauran abokansa sun yi tafiya daga Bichi zuwa Ƙaraye a ranar Talata domin zaman Majalisi.

“Wasu mutane ne a Ƙaraye su ka neme mu domin zuwa Majalisin kuma ya kamata mu koma Bichi a ranar amma sai suka roƙe mu da mu ƙara wasu sa’o’i, ko da yamma ta yi sai suka ce mu kwana a Ƙaraye, in ji Idris.

“Da safe, sai aka rinƙa jinkiri wurin kawo ruwan wanka sai ɗaya da ga cikinmu ya ba mu shawarar mu je kogi mu yi wanka wanda daga nan ne muka soma tafiya.

“Wasu daga cikinmu ba su saki jiki da dam ɗin ba inda suka ce kada mu je saboda wani mummunan abu zai iya faruwa amma sai Musa (yana cikin waɗanda suka rasu) sai cikin wasa ya ce babu abin da zai faru.”

Sai Idris ya ci gaba da bayani kan abin da ya faru a lokacin da suka kai dam ɗin da kuma yadda abokansa uku suka rasu cikin mintoci.

“Dam ɗin yana da ɓangarori biyu, akwai babban wurin wanda muka ƙaurace masa sa’annan akwai ƙaramnin wurin wanda can muka je kuma har muka ga ƙananan yara a wurin da ke wanka.

“Isyaku ne ya soma cire kayansa ya tsunduma cikin ruwan sa’annan Nazifi ya bi shi amma huɗu daga cikinmu sai muka lura cewa ba su fito ba, wanda hakan ya sa Musa ya ce bari ya shiga ya ceto su.

“Ko da Musa ya shiga sai muka lura cewa wani mummunan abu ya faru saboda babu wanda ya fito daga cikinsu sai muka soma ihun kiran mutane.

“Amma abin takaicin shi ne ba a kawo ɗauki da wuri ba saboda bayan minti goma da kusan mutum 20 suka shiga nemansu gawarwakinsu kaɗai aka ciro daga dam ɗin.”

Idris ya ce shi da sauran abokansa ba su iya ruwa ba shi yasa suka yanke hukuncin cewa ba za su shiga neman abokansu ba.

Mahaifin Musa ya bayyana cewa ba zai manta lokacinsu na ƙarshe tare da ɗansa ba kafin suka kama hanyar zuwa Karaye.

“Ina kwance a ɗaki a lokacoin da Musa ya shigo ya gaishe ni ɗauke da jaka inda ya ce mani Baba za mu tafi Karaye domin yabon Annabi ni kuma sai na yi masa addu’ar Allah ya tsare su.”

Mahaifin ya bayyana cewa ba iyalansa kaɗai za su yi kewar Musa ba, a faɗin Bichi ana amfana da shi sakamakon yana da shaguna biyu na POS wanda yake taimakawa domin cire kuɗi.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana reshen Jihar Kano Saminu Yusuf ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ba a tuntuɓe su ba wurin neman ɗauki kuma a lokacin da suka isa wurin masu iyo a cikin ruwa tuni suka ciro gawarwakinsu daga dam ɗin.

Ya bayar da shawara ga musamman baƙi da su guji shiga ruwan da ba su saba da shi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: