Rundunar ƴan sandan Najeriya reshin jihar Kano ta ce abinda ya fashe a ranar Alhamis 17 ga watan Mayu, a wani shago a unguwar Sabon Gari da ke birnin wadda ta hallaka mutum tara, ta faru ne a sanadiyyar wasu sinadarai da ake iya haɗa bam da su.

A lokacin da fashewar ta auku an rika yaɗa labarai kan cewa Bam ne ya fashe a wajan.

A yayinda wasu ke cewa tukunyar gas ce ta mai aikin walda ta fashe a shagon.

Amma cikin tattaunawar da yayi da ƴan jarida, a ranar da abin ya auku, Kwamishinan ƴan sanda na Jihar ta Kano, CP Sama’ila Dikko, ya ce tukunyar gas da ake walda da ita a wajen ce ta fashe, “amma ba bam ne ya tashi ba kamar yadda ake faɗa.”

Bayan gudanar da bincike hukumar ƴan sanda ta fitar da sanarwar ta hannun kakakin ta SP Abdullahi Kiyawa, a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2022.

Rundunar ta ce mutumin da yake gudanar da haramtaccen kasuwancin na sayar da waɗannan haramtattun sinadarai, waɗanda ake haɗa bam da su, da aka gano, Michael Adejo, ya mutu a fashewar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: