Sabon mai kula da ofishin Akanta-Janar na Tarayya (OAGF), Anamekwe Nwabuoku, ana zarginsa da aikata manyan laifukan cin hanci da rashawa, kuma hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa, EFCC, ta na bincikensa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka naɗa Nwabuoku ne domin ya kula da ofishin AGF da aka dakatar, Ahmed Idris, wanda ya shafe sama da mako guda a hannun hukumar EFCC tana binciken badakalar naira biliyan 80 a kansa.

A cewar wata sanarwa da ma’aikatar kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta ƙasa, Nwabuoku zai riƙa kula da harkokin ofishin a lokacin binciken Idris.

Sai dai a cewar wasu rahotanni a ranar Litinin, muƙaddashin AGF ana tuhumar sa da cin hanci da rashawa da suka haɗa da ƙarin albashin da ya yi wa kansa a hukumomin gwamnatin da ya yi aiki a baya.

An kuma yi zargin cewa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa sun kwato wasu kadarorin da ya mallaka ta hanyar damfara.

Ɗaya daga cikin rahotan ya bayyana wa Economic Confidental cewa ɗaya daga cikin laifuffukan kuɗi na Nwabuoku da ake zargin an aikata shi ne a lokacin da yake daraktan kuɗi da asusu (DFA) a ma’aikatar tsaro.

Ana kuma zarginsa da aikata wasu ayyukan damfara da kuma amfani da tsarin gwamnatin tarayya (GIFMIS) wajen satar albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.

GIFMIS shine tsarin tushen IT don sarrafa kasafin kuɗi da lissafin kuɗi. An kuma karɓe shi a matsayin wani ɓangare na dabarun sake fasalin ma’aikatan gwamnati da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi tun farkon shekarun 2000.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa gwamnatin Najeriyar ta zaɓi naɗa Nwabuoku domin kula da ofishin da ake zargin AGF da cin hanci da rashawa, wani babban jami’i a fadar shugaban ƙasar ya ce Nwabuoku ne ya fi kowane mukami a ofishin.

“Ba ya zama mukaddashin AGF amma yana kula da OAGF a matsayin babban darakta a ofishin,” in ji jami’in.

Leave a Reply

%d bloggers like this: