A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da manyan lauyoyin jihohi 36 suka shigar a kan Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NFIU) kan aiwatar da ƙa’idojinta na sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Ƙa’idojin sun takaita adadin da za a iya cirewa daga asusun ƙananan hukumomi zuwa fiye da N500,000 a kullum.

Sai dai masu shigar da ƙara (Gwamnatocin Jihohi) sun yi zargin cewa ƙa’idojin sun saɓawa ƴancin cin gashin kan harkokin kuɗi na jihohi daban-daban kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Saidai Alkalin kotun, Inyang Ekwo, ya ce shari’ar ba ta da inganci.

A cikin ƙarar, babban Lauyan gwamnatin tarayya (AGF), NFIU da kun6giyar ma’aikatan ƙananan hukumomin Najeriya ne ake tuhuma.

Hukumar ta NFIU ta fitar da wasu ƙa’idoji a watan Mayun 2019 domin kare kai daga tasirin da gwamnatocin jihohi ke yi wajen gudanar da rabon ƙananan hukumomi na wata-wata.

Da yake yanke hukuncin, Mista Ekwo ya ce ma’anar ƙa’idojin NFIU shi ne sanya gaskiyar kuɗi a cikin hada-hadar gwamnati a matakin ƙananan hukumomi.

Mista Ekwo ya yarda da AGF cewa ta hanyar sashe na 23 (2) (a), sashe na 28 (2) da sashe na 31 na dokar NFIU, “ɓangarin ta na da ikon yin ƙa’idojin.”

Ƙa’idojin sun yi niyya ne don rage “lalacewar laifuffuka da ake samu ta hanyar fitar da kuɗaɗe daga asusun ƙananan hukumomi a faɗin Najeriya daga ranar 1 ga watan Yuni, 2019.

A ranar 2 ga Maris, lauyan gwamnatocin Jihohin, Omonsoya Popoola, ya ce gwamnatocin jihohin ba su da iko da Hukumar NFIU.

Mista Popoola ya shaida wa kotun cewa ta hanyar gudanar da asusun haɗin gwiwar ƙananan hukumomin jihar, jihohin suna bin dokokin da Majalisar Dokoki ta Jiha ta kafa ba hukumar NFIU ba.

Ya buƙaci kotun da ta bayyana cewa NFIU ba ta da hurumin tsara ƙa’idoji da tsare-tsare da gudanar da asusun haɗin gwiwar ƙananan hukumomin jihar.

Sai dai AGF da Tijjani Gazali, Babban Lauyan Najeriya ya wakilta, ya ce NFIU ba ta kutsa kai cikin ikon jihohi ko ƙananan hukumomi.

“Babu wani abu da ba daidai ba ko sabawa kundin tsarin mulki game da ka’idodin NFIU saboda ba sa amfani da ikon masu shigar da ƙara,” Mista Gazali, daraktan riko na ƙararrakin jama’a a ma’aikatar shari’a ta tarayya, Abuja, ya shaida wa kotu.

Mista Gazali ya ƙara da cewa “a bayyane yake daga tanade-tanaden Dokar NFIU, musamman Sashe na 23 (2) (a) da Sashe na 28 (2) da Sashe na 31 na Dokar NFIU, cewa sashin yana da ikon yin jagororin. ”

Hakazalika, lauyan NFIU, Arthur Okafor, wanda shi ma SAN ne, ya ce hukumar ta yi aiki ne bisa ga hurumin da doka ta ƙayyade don hana cin zarafin ofis da sauran laifukan kuɗi da ka iya tasowa a matakin ƙananan hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: