Ƴan bindiga a safiyar Laraba sun ɓalle ɗaya daga cikin majami’un babban Rabaren na Sokoto, Matthew Hassan-Kukah

Rahotanni sun bayyana cewa, ƴan bindigan ɗauke da makamai sun sace wasu fastoci biyu da wasu mutum biyu a cocin katolika ta St. Patrick, Gidan Maikambo a ƙaramar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Manyan majami’un Kukah sun bazu a jihohin Katsina, Zamfara da Kebbi.

Daraktan sadarwa na Catholic Diocese na Sokoto, Rabaren Christopher Omotosho, ya tabbatar da aukuwar lamarin a safiyar Laraba.

Ya ce an kai farmaki majami’arsu kuma har yanzu babu labarin da suka samu kan inda aka yi da waɗanda aka sace.

Omotosho ya ce, “Da tsakar daren yau, 25 ga watan Mayun 2022, ƴan bindiga sun shiga majami’ar mu ta St. Patrick, Gidan Maikambo, karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

“An sace babban faston Rabaren Fada Stephen Ojapa, MSP, da mataimakinsa Oliver Okpara da wasu yara maza biyu a gidan.

“Har yanzu babu ƙarin bayani kan inda suke. Ku taimaka ku saka su a adu’a domin su dawo cikin aminci.” A cewar sa

A ranar 14 ga watan Mayu, fusatattun matasa masu zanga-zanga sun ƙone tare da tarwatsa cocin da Kukah ke shugabanta a Sokoto bayan ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Deborah Samuel, ɗalibar da ta yi batanci ga Annabi.

Masu zanga-zangar sun ƙone wani daga cikin sashin ginin cocin Kukah kuma sun bankawa wata bas wuta a farfajiyar.

Rikicin addinin na Sokoto ya ƙara gaba inda ya shiga wasu sassan jihohin Bauchi da Abuja a kwanakin da suka gabata yayin da jami’an tsaro da wasu gwamnonin arewa suka ja kunne kan tashin hankula.

Leave a Reply

%d bloggers like this: