Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya (EFCC), ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, mai neman takarar shugaban kasa, a kotu kan zargin almundahanar Naira biliyan 2.3

Okorocha, wanda ke wakiltar Imo ta Yamma a Majalisar Dattawa, an gurfanar da shi ne a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo, a babbar Kotun tarayya da ke Abuja a safiyar yau Litinin.
Hukumar ta kama Rochas a gidansa bayan ta aike masa da takardar gayyata amma ya ƙi amsawa.

Tuni aka cika kotun, inda mutane da dama suka tsaya a yayin da suke jiran fara shari’ar.

Ana gurfanar da tsohon gwamnan ne bisa tuhume-tuhume 17 da suka hada da yin sama da fadi da Naira biliyan 2.9.
An zarge shi da hada baki da wasu da suka hada da dan jam’iyyar APC da wasu kamfanoni biyar domin sata a asusun gwamnatin jihar Jmo, sai dai ya musanta zargin.
Gurfanr da shi a gaban kotun na zuwa ne bayan da ya gaza samun beli daga hannun hukumar.
Rochas ya bayyana bukatar bada belinsa ne a kan cewa shi mai neman takarar shugaban kasa ne, inda ya jaddada cewa burinsa na siyasa zai salwanta matukar ba a bayar da belinsa ba.
Sai dai mai shari’a Ekwo, a wani takaitaccen hukunci da ya karanto a kan neman belin Okorocha a ranar Juma’a, ya ce bai aminta ya bayar da belinsa ba.