A Wani Rahoto da aka Fitar ya tabbatar da cewar Taba Sigari na Hallaka Mutane 29,000 a Najeriya a Kowacce Shekara.

Wani rahota kan tattalin
arzikin kasashen Afrika ya yi nuni da cewa taba sigari na hallaka yan kasa Najeriya 29,000 a kowacce shekara.

Austin Iraoya na daga cikin masu gudanar da binciken ya ce yan Najeriya na kashe kudade sama biliyan 526 na taba sigari da kuma nema mata magugunan cutukan da taba ke haifarwa rayuwar Dan’adam.

Sannan ya ce wannan al’amari na yiwa tattalin arzikin kasa babbar illa.

Ya ci gaba da cewa Gwamnatin Najeriya na samun kashi 10 cikin 100 na wadannan makudadan kudaden da ake kashewa a duk shekara.

Rahoton na zuwa ne lokacin da ake gudanar da ranar yaki da taba sigari ta Duniya wadda aka gudanar a jiya Litinin a babban Birnin tarayyar Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: