wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a safiyar yau Litinin sun kai hari a jerin gidaje na Gwarinpa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Rahotani sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kai hatin a rukunin gidajen tsakanin karfe 1 na dare zuwa karfe 4 na asuba, sanna suka yi awon gaba da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Wani mazaunin garin mai suna Mohammed ya ce ‘yan bindigar sun samu shiga yakin gidajen Genuine katin shiga na Efab Queens da ke lamba 6th Avenue, Gwarinpa.

Cikin zantawa da shi ta wayar tarho ya bayyana cewa ’yan bindigar na dauke da baka, da kibiyoyi, da adduna kuma suna da yawa.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta shaida cewa ƴan fashi ne su ka kai harin ba masu garkuwa ba.
Josephine Adeh ta ce tuni aka tura ‘yan sanda zuwa wurin domin sanin yadda layanin ya faru da nemo mafita.
Ta ce a nan gaba za su fitar da cikakken bayani bayan kammala bincike.