Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naganawa da gwamnonin Arewa a kan fitar ɗan takarar shugaban ƙasa.

Shugaban ya shiga tattaunwa da gwamnonin arewa na jam’iyyar APC domin tattauna batun ɗan takar da ake gab da gudanar da zaɓe a jam’iyyar.

Ganawar na zuwa ne bayan da ake shirye-shiryen gudanar da zaɓen fidda gwani don fitar da ɗan takara.

Gamnonin da su ka halarta akwai Gwamna Kano, Abdullahi Ganduje, gwamna Neja, Abubakar Sani Bello da gwamman jihar Borno Babagana Umara Zulum.

Sauran su ne Malam Nasir El’rufa’i da Gamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule,  gwamnan jihar katsina Aminu Bello Masari sai gwamnan jihar Kwara Abdurrahman Abdurrazaƙ.

Haka kuma akwai gwamna jihar Plateau Simon Lalong, da gwamnan jihar Gombe Mohammed Inuwa Yahaya sai gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru sann gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu.

A na sa ran ganwar za ta mayar da hankali ne a kan batun fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: