Akalla kwamfutoci 100 ne suka salwanta sakamakon wata gobara da ta tashi a Sashen Nazarin Kwamfuta na Kwalejin Ilimi da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Jami’an kashe gobara sun yi kokarin kashe wutar da ta tashi da misalin karfe 9 ja safiyar Asabar, lokacin da ma’aikatan kwalejin su ke hutun ƙarshen mako.
Shugaban Kwalejin, Dokta Suleiman Balarabe, ya ce wutar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki, wanda hakan ya shafi kayan aikin sashen.

Ya kara da cewa, yana daga cikin tsarin Kwalejin na kashe kayan wutar lantarki a duk lokacin da aka tashi daga aiki, amma ya bada tabbacin za a musanya na’urorin da suka kone da wasu.

Haka kuma ya ce sun dauki matakin kauce wa sake faruwar hakan a gaba.
Ya ce zasu sa a fito da wasu kwamfutoci da hukumar TETFund ta basu a baya don bai wa dalibai damar ci gaba da amfani da su na wucin gadi kafin lokacin da za a gyara sashen da ya kone.
Shugaban ya yaba wa hukumar kashe gobara ta jihar da sauran waɗanda su ka bayar da gudunmawa don kashe gobarar.
Sai dai babu rahoton rasa rai ko jikkata a sanadin gobarar.