Wata ‘yar kasuwa da ke zaune a jihar Legas ta rasa ranta bayan ta garkame kanta a bandaki yayin da jami’an Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa (EFCC) suka yi yunkurin kama ta.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a ranar Lahadi.

Ya ce lamarin ya auku ne ranar 2 ga watan Yuni a gida mai lamba 15 layin Dele Onabule na Magodo Brooks cikin Legas.

Hundeyin ya bayyana yadda jami’an EFCC suka dira gidan matar don su kama ta don gudanar da bincike.

A cewarsa, matar mai suna Olufunmbi Jaiyeola ta ki yi wa jami’an iso zuwa cikin gidan na tsawon awanni.

Kakakin ya ce daga bisani jami’an sun samu damar shiga gidan tare da taimakon wani ‘dan uwanta.

Sai dai, an gano yadda Jaiyeola ta garkame kanta a bandakinta kuma ta rasa ranta a ciki.

Hundeyin ya ce hukumar EFCC sun shiga don su kama ta, amma suka ga bakin matar ya na kumfa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: