Yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa sun isa wajen domin sanya idanu a kai.
Hukumar ta aike da jami’anta wajen da ake gudanar da zaɓen domin sa ido wajen hana maguɗi ko siyan ƙuri’a.
Ko a zaɓen fidda gwani da ya gudana a jam’iyyar PDP a baya, sai da hukumar ta isa wajen domin sa ido a kai.
A na gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jam’iyyar APC a filin wasa na Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanni daga Abuja na nuni da cewar wani daga cikin masu zaɓen a jihar Jigawa ya rasa ransa yayin da ake shirye-shiryen fara zaɓen.
Tun a baya ƙungiyar gwamnonin arewa na jam’iyyar APC su ka nuna ƙin amincewa da bai wa ɗan arewa damar mulkin ƙasar tare da jaddada buƙatarsu na miƙa mulkin zuwa kudancin Najeriya.
Ƙungiyar ta aike da sunayen ƴan takaraa biyan daga kudancin Najeriya da su ka fi buƙata a tsayar a zaben fidda gwani da ake gudanarwa a yau Talata.