Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.
Bola Tinubu ya lashe zaɓen da ƙuri’u 1,271 kuma haka ne mafi yawa daga cikin ƙuri’un da daliget su ka kaɗa.
An fara zaɓen ne a jiya Talata yayin da wasu daga cikin ƴan takarar su ka janye masa.