Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaron kasar nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ana sa ran taron zai tattauna batutuwan da suka shafi dabarun bunkasa nasarorin da aka samu a baya-bayan nan wajen yaki da ta’addanci da rashin tsaro gaba daya.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

A gefe guda akwai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojoji, Laftanar Janar Farouk Yahaya,Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo, da babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao suma sun halarci taron.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman, Babban Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi, da Darakta Janar na Hukumar Leken asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: