Akalla mutane 65 ne suka rasa rayukan su yayin da wata annoba ta ɓarke a Jihar Jigawa.

Cutar wadda ta fara a watan da ya gabata ana ganin cutar ta yaɗu zuwa fadin ƙasa Najeriya gaba ɗaya.
Wasu mazauna ƙauyuka sun bayyana cewa mutane da dama na garuruwan sun rasa hankalin su wasu kuma Jin su.

Sannan yankunan da alamarin yafi kamari shine Dungundun Kenya ArewaDantsanoma Babura Gumel da karamar hukumar Suletankarkar .

A wani rahoto ya nuna cewa mutane 100 cutar ta kashe yayin da 360 su ka kamu da ita a Jihar ta Jigawa
Mai garin Dungundun Malam Alkasin Yakubu ya bayyana cewa sun rasa mutane 19 a wanann garin mafi yawa yara ne ƙanana.
Ya ci gaba da cewa cutar ta ɓarke a watan da ya gabata kuma ta fi kamari ƴan kwanakin nan na mace_mace da kumuwa.
Yakubu ya ce mutane 19 sun mutu biyu sun rasa hankalin su da kuma Jin su, ganin abun da ba su sani ba ya faru, sannan sun daukar matakin gaggawa zuwa asibitin Gumel tare da tabbatar da rasuwar su , sannan wasu sun mutu a gidajen su kafin a akai su zuwa asibiti.
Shima mai garin Babura Alhaji Akilu Dawaki ya ce 19 ne suka rasa rayuwar su tare da samun Sabbin kamuwa 70.
Da mu ka tuntubi ma’akatar lafiya ta Jihar ta tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce akalla mutane 65 ne suka mutu 257 ke dauke da cutar cikin kanannan hukumomi 27 na jihar