Kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ASUU ta yi watsi da tayin tallafin naira miliyan 50 da aka yiwa kungiyar domin ta janye daga yajin aikin da ta tsunduma.

Jagororin kungiyar sun bayyana cewa ba za su amshi kudaden da mutane su ka yi karo-karo domin su biya musu bukatun su.
A safiyar yau Asabar ne dai kungiyar ta ki amincewa a lokacin da kungiyar ta karbi bakuncin kungiyar shirin Brekete Family wanda gidan redio Human Right ke gabatarwa a Birnin tarayya Abuja.

A lokacin da za a gudanar da shirin gidan rediyo ta samu nasarar gayyatar shugaban kungiyar ta ASUU Farfesa Emmanuuel Osodeke da kuma ‘yan kungiyar domin yin bayani dangane da kin komawar malaman bakin aiki.

Mai gabatar da shirin Ahmad Isah shine wanda ya kafa asusun wanda aka tarawa kungiyar kudaden domin ta janye daga yajin aikin da ta ke ciki.

Tun kafin gidan rediyon ya gayyato kungiyar ta ASUU mai gabatar da shirin Ahmad Isah ya gabatar da naira miliyan 50 ga gwamnatin Jihar Akwa-Ibon domin ya sanya a asusun tallafi wanda aka bude a banki.

Bayan an gabatar da kudaden a gaban mutane shugaban kungiyar ta ASUU ya ki amincewa da kungiyar ta karbi kudaden.

A lokacin da kungiyar ta ASUU ta ki yarjewa ta karbi kudaden Ahmad Isah ya bayyana cewa zai soke gidauniyar da ya kafa tun da kungiyar ta ASUU ba karbi kudaden ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: