Babbar kotun jihar Kano da ke zaune a Audu Baƙo ta sanya ranar 28 ga watan Yulin da mu ke ciki domin yanke hukunci a kan shari’ar mutanen da ake zargi da kisan ɗaliba Hanifa Abubakar.

Alƙalin kotun Usman Na’abba ne ya tsayar da ranar yayin zman kotun a yau Talata.

A na zargin Abdulmalik Tanko da wasu mutane biyu da haɗa kai da yin garkuwa, cin zarafi da kuma kisan ɗaliba Hanifa mai shekaru biyar a duiya.

Sai dai wanda ake zargi da aikata laifin ya musanta tare da bayyana cewar tilast shi aka yi ya amsa laifin da bai aikata ba.

An gurfanar da Abdulmalik Tanko, da Fatima Jibril sai Hashim Isyaku a gaban kotun bayan da jami’an staro su ka kama su.

Tun a ranar 4 ga watan Disamban shekarar 2021 aka yi garkuwa da Hanifa Abubakar daga bisani kuma aka gano waɗanda su ka yi garkuwa da ita tare da neman kuɗin fansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: