Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar kama wasu ‘yan bindiga uku a kusa da kasuwar mata da ke cikin sabon garin Zariya a Jihar.

Jami’an tsaron ‘yan sandan sun cafke mutanen ne a lokacin da jami’an su ka kai farmaki unguwar Jaba bayan da su ka samu bayanan ‘yan bindigan sun shiga yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan shigar ‘yan bindiga yankin sun kutsa kai cikin gidajen mutanen a ranar juma’a zuwa wayewar Asabar.

Jami’an na ‘yan sandan sun cafke mutanen ne a lokacin da su ka nufi cikin daji har ta kai ga sun samu nasarar cimma batagarin.

‘Yan sandan sun kutsa cikin dajin kuma ‘yan sandan sun harbi wasu mutum biyu daga cikin ‘yan bindigan amma sun tsere.

Jami’an sun kuma samu nasarar kwato wayoyin hannu guda shida da babura guda biyu.

Bayan kwato baburan, jami’an ‘yan sandan su ka sake komawa cikin dajin harta kai ga sun isa mafakar ‘yan bindigan inda su ka kama mutane uku a cikin dakin su.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda Jihar DSP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar Lamarin, inda ya ce jami’anna su su na ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran yan bindigan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: