Wasu da ake kyauta zaton yan bindiga ne sun abka asibitin koyarwa na jami’ar Osun domin kuɓutar da gawar wani ɗan uwansu da aka kashe.

Maharan sun abka tsakiyar asibitin ne domin kuɓutar da ɗan uwan nasu da ya samu munanann rauni daga bisani kuma ya mutu.

Rahotanni sun ce mutane biyu ne su ka mutu yayin da ƴan bindigan su ka fafata faɗa Osogbo ranar Talata.

Wani da al’amarin ya faru a kan idonsa ya shaida cewa, ƴan bindigan sun shiga asibitin ɗauke da muggan makamai sannan suka fara harbin iska lamarin da ya ranazana ma’aikatan asibitin.

Bayan da ƴan bindigan su ka buƙaci a basu gawar ɗan uwansu ma’aikatan su ka ƙi, hakan ya sa su ka fara harbin iska domin kubutar da gawarsa.

Shugaban asibitin koyarwa na jami’ar jihar Babatunde Afolabi y tabbatar da faruwar lamarin yayin da ya ke yi wa manema labarai ƙarin bayani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: