Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba zai janye wa kowa takararsa ba har da yan takarar manyan jam’iyyun APC da PDP, wato Bola Tinubu da Atiku Abubakar.
Sanata Kwankwaso ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP ya musanta raɗe-raɗin da ake kan cewar zai janyewa ɗaya daga cikun manyan jam’iyyun ƙasar.
Jagoran na Kwankwasiyya ya bayyana hakan ne cikin wata hira ta musamman da ya yi da wakilin Jaridar The Punch.
Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce tafiyar Kwankwasiya ta bazu dukkan sassan Najeriya kuma ya yi farin cikin ganin an rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe don hakan na nufin zai yi wuya a murde zabe kamar yadda aka saba yi a baya.
Kwankwaso ya ce muddin za a yi zabe na adalci, zai yi wahala wani ya doke su, ya ce ya na da tabbacin samun nasara a kan dan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu da na PDP, Atiku Abubakar a zaben 2023.
Yayin da ya ke amsa tambaya kan yiwuwar janye wa Atiku a zaben don kayar da APC, ya ce
Sanata Kwankwaso ya ce ba zai janye wa kowa ba, jam’iyyar su ta NNPP ta yi fice a dukkan sassan kasar nan, kuma sh na da tabbacin za su ci zabe.
Jagoran ya ce baya ganin Tinubu da Atiku a matsayin kalubale domin ba shi ne zai kada su ba, talakawan Najeriya ne za su kada su saboda sun yarda da jam’iyyar NNPP.