Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta tsige shugabsan majalisar Prince Matthew Kolawole sa’o’i kadan bayan da majalisar ta tsige mataimakin shugaban majalisar Ahmad Muhammad da kuma wasu shugabannin majalisar su uku.

‘Yan majalisar Jihar ne su ka fitar da wasikar tsige shugaban majalisar a lokacin da su ka sanyawa wasikar hannu kan zargin yin sama da fadi da wasu kudade sakamakon sakaci da aikin sa.

‘Yan majalisar 19 wanda su ka tsige shugaban sun bayyana cewa shugaban majalisar ya ki biyan su kudaden su tun a shekarar 2019 da ta gabata.

Sannan sun kara da cewa baya ga yin sama da fadi da kudaden Kolawale ya kuma karbi bashin kudadi na miliyoyin Nairori da sunan majalisar.

‘Yan majalisar sun ce tsigewar da su ka yiwa Priss Kolawale za ta fara aiki ne tun a ranar 13 ga watan Yunin da mu ke ciki.

Sun kuma ce sun gano shugaban majalisar ya na daukar muryoyin su ba tare da sanin su ba yana kai wa gwamnan Jihar domin ta yar da fitina.

Anasa bangaren shugaban Majalisar Priss Kolawole ya ce tsige shi da ‘yan majalisar su ka yi ya dauke shi ne amatsayin rashin aikin yi.

Sakataren yada labaran shugaban ya bayyana cewa bayyana tsige shugaban da ‘yan majalisar su ka yi haramtacce ne.

A bangaren mataimakin shugaban ‘yan majalisa 17 ne su ka amince da tsige shi a takardar da su ka sanyawa hannu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: