A wani Rahoto da cibiyar tsaro da bincike ta security tracker ta yi ta ce, mutane 3,478 aka hallaka a Najeriya tare da yin garkuwa da 2,256 tsakanin watan Disaambar shekarar 2021 zuwa watan yunin shekarar 2022.

Cikin rahoton da aka fitar ya nuna cewa a watan Disamba an kashe mutane 342 sanann an yi garkuwa da mutane 397 sai wasu manoma 45 da aka yi garkuwa da su a jihar Nassarawa.

Sanann a watan Junairu an kashe mutane 844 tare da yin garkuwa da wasu 603.

Kuma cikin manyan jihohin Arewacin Najeriya an kashe mutane sama da 400 a Kowacce jiha daga ciki.

Sannan mafi yawan hare-haren an fi kaiwa Arewacin Najeriya kuma aka fi kashewa duk da dai a kudancin kasar akwai kungiyar IPOB itama ta na kai hare-hare.

Cibiyar ta ce hare-haren Arewa maso yammaci ya fi ta’azzara ga jihohin Neja, Kaduna, Katsina, Sokoto, Zamfara wanda ake ganin barayin daji ne da masu garkuwa da mutane su ke kai hare-haren.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: