Ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya ta bai wa mambobinta umarnin fara sayar da lita ɗaya naira 180.

Shugaban kungiyar masu sayar da mai a Najeriya ne ya bayyana cewa kungiyar su ba za ta iya sayar da man fetur a kan kuɗi naira 165 kamar yadda Gwamnati ta bayyar da umarni ba.

Akinrinde ya bayyana haka ne a wata hira da akai da shi a gidan talabiji na channel a jiya Litinin.

Ya ce man fetur ya na wahala a kasar nan musamman ma Abuja da Legas sannan kowanne dan kasuwa ya kan siyo man akan kudi naira 175 zuwa 178 Kowacce lita.

Sannan su kan yi safarar sa zuwa Jihar da za a kai shi yanayin kudin yanayin nisan Jihar.

Amma kuma gwamanti ta na so ta tirsasa su su sayar da shi 165 lita daya.

Don haka kungiyar su ta IPMAN ba za su iya siyar da mai naira 165 shi ya sa su ka rufe gidajen man su.

Sannan mambobin kungiyar su ta IPMAN sun rufe gidajen man su ba da nufin tafiya yajin aiki ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: