Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi ƙasar Rwanda don tattauna makomar mutane biliyan biyu da ke rayuwa a ƙasashe masu cin gashin kansu.

Taron zai samu halartar shugabannin mafi yawan ƙasashen duniya musamman na nahiyar Afrika, Amuruka, Asia da Europe da Pacific.
Ƙasashen da ke ƙarƙashin nahiyar na ƙungiyar ƙasashe rainon ingila kuma taron an masa take da CHOGM 2022.

Za a tattauna makomar mutanen da ke rayuwa a ƙasashe 54 na faɗin duniya musamman na kasashe rainon ingila, da kuma batun tattalin arziƙi da batun haƙƙin ɗan’adam.

Ƙasashen da su ka shafa akwai a nahiyar Afrika da Asia, Europe, Amerika.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya sanyawa hannu, ya ce shugaban ya samu rakiyar ministoci sauran muƙarrabai a gwamnatinsa.
Daga cikin ministocin akwai ministan sadarwa, ministan harkokin ƙasashen waje da ministan ministan lafiya da kinistan muhalli sai ministar kasafi da tsare-tsare.
Haka kuma akwai shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa, da mak bai wa shugaban ƙasa shawara a kan harkokin tsaro kuma ake sa ran za su koma Najeriya ranar Lahadi.