Connect with us

Labarai

Ƴan Sanda A Zamfara Sun Kuɓutar Da Jarirai Daga Hannun Ƴan Bindiga

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar kuɓutar da jaridai biyu da wasu mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Mutanen su 14 a na zargin sun shafe fiye da kwanaki 40 a hannun yan bindiga.

Mai magana da yawun ƴan sandna jihar SP Muhammad Shehu ya ce sun ceto mutanen ne a wurare daban-daban da yan binsigan su ka killace su.

Kakakin ƴan sansan ya ce jariran biyu kowannensu shekararsa ɗaya.

Bayan samun bayanai a kan maɓoyar masu garkuwa da mutanen ƴan sanda haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun nufi karamar hukumar Tsafe tare da yi wa dajin Kunchi Kalgo ƙawanya tare da farwa yan bindigan.

Daga bayanan da utanen da aka kubutar su ka bayyana sun ce yan bindiga sun kai wani hari Nassarawar Wanke da ƙauyen Rijiya a karamar hukumar Gusau sannan su ka sace mutanen.

Kwamishinan yan sandan jihar Ayuba Elkanah ya danƙa mutanen ga yan uwansu sannan ya ce za su ci gaba da haɗa kai da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

 

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Bayelsa Ta Kwashe Watanni Uku Babu Wuta – Diri

Published

on

Gwamnan Jihar Bayelsa Douye Diri ya tabbatar da cewa watanni uku kenan Jiharsa ba ta samu hasken wutar lantarki ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, a gurin taron Editocin Kasar nan na shekarar 2024, wanda aka gudanar a garin Yenagoa babban birnin Jihar.

Diri ya kara da cewa Jiharsa ta fada cikin duhun rashin wutar lantarki ne, bisa lalata na’u’rorin wutar lantarkin na Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Kasa TCN.

Acewar gwamnan tun bayan lalata na’u’rorin samar da wutar da batagari suka yi, Jihar ta fada cikin duhun na tsawon watanni uku.

Gwamnan Diri ya ce a halin yanzu gwamnatinsa na aikin hadin gwiwa da kamfanin na TCN domin gyara wutar Jihar.

Inda ya ce hakan na daya daga cikin manufofinsa, kuma zai yi kokarin ganin ya samarwa da Jihar, injina masu amfani da gas domin Jihar itama ta tsaya da kafafunta.

Continue Reading

Labarai

Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna Ta Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu masu garkuwa da mutane Uku a Jihar, tare da kwato makamai.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar ASP Mansur Hassan ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Kakakin ya ce jami’an rundunar na Operation Fushi Kada ne suka kama mutane, wadanda suka kasance ‘yan wata kungiyar masu garkuwa da mutane ne, wadanda suka addabi matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja, tare da Jihohin da ke kusa da Jihar.

Mansur ya ce wadanda aka kama sun hada da Muhammad Lawal Abubakar, Abubakar Isah, Samaila Sai’du, inda kuma aka kamasu bayan samun bayanan surri akansu.

Kakakin ya kara da cewa jami’an sun ƙwato bindiga kirar AK-47, da jigida wadda babu komai a cikinta, inda kuma a halin yanzu wadanda aka kama na taimakawa jami’an da bayanan da za su taimaka wajen kama sauran ‘yan kungiyar.

Continue Reading

Labarai

‘Yan Sanda A Katsina Sun Dakile Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane A Jihar

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta samu nasarar dakile, wani harin da ‘yan bindiga su kai yunkurin kai’wa karamar hukumar Jibia ta Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Abubakar Sadik Aliyu ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar juma’ar nan.

Ya ce rundunar, tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro ne suka kubtar da mutane 21 da aka aka yi yunkurin garkuwa da su.

Kakakin ya ce maharan sun kai hare-haren ne a unguwannin Ka’ida, Unguwar One Boy da kuma Danmarke a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 9:15 na dare.

Sadik ya bayyana cewa bayan samun rahotan afkuwar hakan, suka aike da jami’an tsaro, gurin karƙashin Bature ‘yan sandan yankin na Jibia, inda suka daƙile harin bayan yin musayar wuta da maharan na sama da sa’a ɗaya.

A cewar Kakakin musayar wutar tsakanin bangarorin biyu ta sanya maharan tsereww dauke da raunuka a tare da su.

Sai dai ya ce mamba ɗaya na rundunar sa-kai ta KSWC a Jihar, da wani dan sanda ɗaya sun rasa rayukansu a lokain musayar wuta.

Abuakar Sadik ya kuma ya ce, wasu karin mutane biyar da aka ceto,sun jikkata, inda aka kaisu asibiti domin ya musu ak.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: