Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu yayin da gidaje 2,250 suka hallaka sanadiyyar wata Ambaliya da mamakon ruwan sama a ƙananan hukumomi biyar na jihar Kano.

Shugaban hukumar kai ɗaukin gaggawa ta jihar Kano, SEMA, Dakta Sale Jili, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.

A cewarsa, ƙananan hukumomin da lamarin Ambaliyar ya shafa sune, Rano, Kibiya, Doguwa, Danbatta da kuma Kiru.

Bayan aukuwar wannan lamarin, Dakta Sale Jili, ya shawarci baki ɗaya mutanen da ke zaune a dukkan sassan Kano su samar wa ruwa hanya ta hanyar gyara hanyoyin Lambatu da ke gaban gidajen su.

Ya ce Hukumar kula da hasashen yanayi (NiMeT) ta bayyana hasashenta na ruwan sama a daminar bana 2022, inda ta yi hasashen saukar ruwan sama mai tsanani a jihar Kano.

Bugu da ƙari, Dakta Saleh ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ba zata yi ƙasa a guiwa ba a kokarin da take na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: