Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredelu ya sake yin Kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya do amincewa da kafa yan sandan Jihohi a fadin kasar.
Rotimi ya bayyana haka ne a yayin wani taro mai taken rashin tsaro cin hanci da rashin tabbatar damakwaradiyya wanda aka gudanar a jiya Lahadi.
Ya ce Samar da yan sandan Jihohi ne kawai zai kawo karshen duk irin matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a fadin kasar.
Akeredulu ya ce duba ga yadda lamarin tsaro ke kara ta’azzara a kasar samar da yan sanda Jihohi shi ne mafita kuma ya yi kira ga Gwamnatin tarayya ta karbi wannnan tsarin domin shine mafita ga yan Najeriya.
Gwamnan Rotimi Akeredulu ya ci gaba da cewa a duba shari a da dokokin kasa abune mai kyan gaske ga yan kasa,
Sannan ya kamata gwamnoni su taya shi roƙon gwamnatin tarayya domin cika wannan kudiri.