Daga Yahaya Bala Fagge

 

 

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantar sakandire a Najeriya NECO ta sauya ranar Asabar 9 ga watan Yuli a matsayin ranar rubuta jarrabawa.

Mai magana da yawun hukumar Azeez sani shine ya bayyana haka inda ya ce babu jarrabawa a ranar Asabar yayin da ake shirin bikin Sallah.

Sani ya ce hukumar NECO ba ta sanya ranar Asabar a matsayin ranar rubuta jarrabawa ba.

Sannan ya ce sun bai wa ɗaliban hutun mako guda lokutan bukukuwan sallah domin gudanar bmda bukin sallah.

Ya ci gaba da cewa hukumar ta na daukar komai da mahimmanci shi ya sa ba za ta bari hakan yana faruwaba, kuma NECO tana duk mai yiwuwa wajen sanya dalibai farin ciki.

Mai magana da yawun hukumar ya ce ya na amfani da wannan damar wajen fadawa daliban dake rubuta jarrabawar NECO cewa an fara rubuta jarrabawar a ranar 27 ga watan Yunin da ya gabata sannan za a kammala ranar 12 ga watan Augusta shekarar 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: