Yayin da ake ci gaba da samar da hanyoyin nishadantar da masu kallo, kamfanin Blue Sound Multimedia ya haska tallan wasan wkaikwayon da ya samar mai suna Lulu Da Andalu.

Sabon shirin wanda ya tara ƙwararrun jarumai maza da mata, da ma sabbin jarumai da ma’aika masu fasaha domin ganin an ƙirƙiri abubuwa masu ƙayatarwa a cikinsa.

Wanda ya shirya shirin TY Shaba ya bayyana cewar sun shirya shirin ne baya bibiyar tarihi tare da nunw jama’a yadda mutane ke alaƙa da aljanu tun a baya.

Yayin da aka shirya taron nuna tallan shirin wanda aka gayyaci manyan ƴan jarida da ƙararru a ɓangaren, wasu daga cikin waɗand su ka kalla sun bayyana shirin a matsayin wani mataki d zai sauya alƙibilar masana’antar fina-finan Hausa.

Wasu daga cikin waɗanda su ka taka rawa a cikin shirin sun bayyana wa masu kallo rawar da su ka taka a ciki tare da tabbatar da cewar shirin zai kayatar fiye da yadda ake tunani.

Sabon shirin  ya samu aikin bayar da umarni daga Kamilu Ɗn Hausa y ace wannan aikin ya  ƙunshi sabbin hnyoyi na zamani wanda za su ƙayatar da masu kallo a ckin sa.

Jarumai da masu bayar da umarni da ma masu shirya fina-finai ne su ka halarci ɗakin nuna fina finai na Pltinium a ranar Juma’a domin kallon tallan shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: