Connect with us

Labarai

Lulu Da Andalu – Sabon Shiri Domin Juya Akalar Kannywood

Published

on

Yayin da ake ci gaba da samar da hanyoyin nishadantar da masu kallo, kamfanin Blue Sound Multimedia ya haska tallan wasan wkaikwayon da ya samar mai suna Lulu Da Andalu.

Sabon shirin wanda ya tara ƙwararrun jarumai maza da mata, da ma sabbin jarumai da ma’aika masu fasaha domin ganin an ƙirƙiri abubuwa masu ƙayatarwa a cikinsa.

Wanda ya shirya shirin TY Shaba ya bayyana cewar sun shirya shirin ne baya bibiyar tarihi tare da nunw jama’a yadda mutane ke alaƙa da aljanu tun a baya.

Yayin da aka shirya taron nuna tallan shirin wanda aka gayyaci manyan ƴan jarida da ƙararru a ɓangaren, wasu daga cikin waɗand su ka kalla sun bayyana shirin a matsayin wani mataki d zai sauya alƙibilar masana’antar fina-finan Hausa.

Wasu daga cikin waɗanda su ka taka rawa a cikin shirin sun bayyana wa masu kallo rawar da su ka taka a ciki tare da tabbatar da cewar shirin zai kayatar fiye da yadda ake tunani.

Sabon shirin  ya samu aikin bayar da umarni daga Kamilu Ɗn Hausa y ace wannan aikin ya  ƙunshi sabbin hnyoyi na zamani wanda za su ƙayatar da masu kallo a ckin sa.

Jarumai da masu bayar da umarni da ma masu shirya fina-finai ne su ka halarci ɗakin nuna fina finai na Pltinium a ranar Juma’a domin kallon tallan shirin.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Gwamnatin Kaduna Za Ta Tallafawa Yara Masu Zanga-zanga Na Jihar Don Dogaro Da Kansu

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bai’wa kananan yaran da aka kama a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a Kasar na Jihar tallafin naira 100,000 kowannensu.

Sakataren gwamnatin Jihar Abdulkadir Mu’azu Meyere ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a yau Laraba bayan sakin yaran da aka yi.

Ya ce gwamnatin ta Kaduna za kuma bai’wa yaran tallafin domin ganin sun fara kasuwanci, wanda hakan zai canja halayensu zuwa nagari.

Sakataren ya ce gwamnatin Jihar ta Kaduna za ta sanya idanu akan yaran su 39 domin ganin sun koma mutanen kirki.

Acewarsa gwamnatin Jihar ta kuma tattara dukkan bayanan yaran, da inda suke zaune da lambobin wayarsu da sunayen iyayensu domin bibiyarsu akai.

Kazalika Mu’azu ya kuma ce an yiwa yaran gwaje-gwajen lafiya, da kuma nuna musu muhimmancin zama mutanen kirki, inda ya ce bayan da dawo da yaran Jihar tu ni aka miƙa su ga iyayensu.

Continue Reading

Labarai

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Neja

Published

on

Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka wasu manoma kimanin Goma, tare da yin garkuwa da wasu da dama a Karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Maharan sun kai harin ne a jiya Talata a Kauyukan Wayam da Belu-Belu da ke cikin Ƙaramar Hukumar a lokacin da mutanen kauyen ke gabatar da sallar Asuba.

Daga cikin wadanda maharan suka hallaka ciki harda wasu mata.

Wasu mazauna yankin sun ce maharan sun hallaka mutane shida ne daga cikin wadanda suka hallaka ta hanyar sare musu kai, yayin da suka jikkata wasu da dama a cikin kauyukan biyu.

Wani mazaunin yankin mai suna Bala Tukur ya ce da yawa daga cikin mazauna yankin sun tsere, bayan aika-aikar da maharan suka yi a kauyan, wanda hakan ya kuma kawo nakasu a girbe amfanin gonarsu.

Tukur ya kara da cewa maharan na kuma sanyawa mazauna yankin biyan kudin haraji kafin shiga gonakinsu a lokacin girbe amfanin gonarsu da suka shuka.

Har ila yau Maharan sun kuma sa ke kai wani hari garin Zungeru duk da ke Jihar, inda suka yi garkuwa da mutane da dama, ciki har da wasu ‘yan Kasar India biyu da ke aiki a gonar shinkafa a Borgu da ke Jihar.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida na Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed ya ce gwamnatin jihar na sane da hare-haren ‘yan bindigar ke kai’wa a JIhar kuma za ta dauki mataki.

Continue Reading

Labarai

Kungiyar Gwamnonin Arewa Sun Mika Sakon Ta’aziyya Ga Tinubu Bisa Rasuwar Babban Hafson Sojojin Kasar

Published

on

Kungiyar gwamnonin Arewa sun mika sakon ta’aziyya ga shugaban Kasa Bola Tinubu bisa rashin babban hafson sojin Najeriya Laftanal-Janar Taoreeed Lagbaja.

Kungiyar ta kuma mika sakon ta’aziyyar ta ga Rundunar sojin Kasar bisa rashin Lagbaja da aka yi a Kasar.

Kungiyar ta mika sakon ta’aziyyar ne ta cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Ismaila Uba Misilli a yau Laraba.

Kungiyar gwamnonin ta bayyana marigayin a matsayin gwarzon soja da ya hidimtawa Najeriya a lokacin da ya na raye.

Kungiyar ta ce Janar Lagbaja ya sadaukar da rayuwarsa ne ga rundunar sojin Kasar, domin ganin an tabbatar da martabar Najeriya duk da ƙalubalen da ake fuskanta na ‘yan ta’adda a Kasar da sauransu.

Shugaban kungiyar gwamnoni ya kuma mika sakon ta’aziyyarsu ga matar marigayin, Mariya Lagbaja, da ‘ya’yansa biyu ,inda Matar tasa ta Kasance ‘yar asalin Jihar Gombe a karamar hukumar Kaltungo.

Kungiyar gwamonin Arewan sun kuma sake mika sakon ta’aziyyarsu ga gwamnatin Tarayya da al’ummar Jihar Osun mahaifar marigayin.
Lagbaja ya mutu ne a jiya Talata bayan fama da rashin lafiya a Ketare, kuma ya rasu ne yana da shekara 56 a duniya.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: