Aƙalla mutum 18 ne suka rasa rayukan su a safiyar ranar Lahadi bayan wasu ‘yan bindiga sun farmaki ƙauyukan Kango da Ɗangulbi na ƙaramar hukumar Maru a Zamfara.

Rahotanni sun cewa mazauna ƙauyukan sun tabbatar da haka, inda suka ce da yawan mutanen ƙauyukan sun tsere yayin harin kuma har yanzy ba su koma ba.
Ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara na ɗaya daga cikin yankunan da ayyukan ta’addancin yan bindiga ya fi muni a jihar.

Wani mazaunin cikin garin Maru, Shehu Ismaila, ya ce an kashe bayin Allah 13 a ƙauyen Dangulbi yayin da wasu aka kashe wasu mutum biyar a ƙauyen Kango.

Sama’ila wanda asalinsa ɗan ƙauyen Ɗangulbi ne ya ce maharan sun kai hari Kango ne da farko kafin daga bisani su zarce ƙauyen Ɗangulbi, inda suka kashe manoman da ke aiki a gonakin su.
Shehu Sama’ila ya kara da cewa ƙasurgumin ɗan bindigan, wanda ake kira da Damina ya nemi miliyan biyu daga ƙauyen Ɗangulbi a matsayin harajin kariya, sai dai mutane sun gaza haɗa kudin saboda halin da ake ciki.
Yayin da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda na Zamfara, Mohammed Shehu, bai ɗaga kiran waya ba kuma bai dawo da amsar sakonnin da aka tura masa ba dangane da harin.