Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya taya Sen. Kashim Shettima murnar tsayar da shi takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana Shettima a matsayin mai saurin fahimta kuma ya cancanci zama a ofishin mataimakin shugaban kasa.
Ganduje ya bayyana cewa, a lokacin zaben fidda gwanin da ya gudana, Shettima ya taka muhimmiyar rawa kuma ya nuna cancantar sa.

Ganduje ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa wakilin mazabar Borno ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Borno da ya yi wa’adi biyu zabi ne mai kyau da zai iya yin aiki tare da dan takarar shugaban kasa domin kai Najeriya ga wani matsayi mai girma.

Gwamnan ya yabawa dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, kan zabin da ya yi a Shettima, ya kuma bayyana hadewar a matsayin tabbacin samun nasarar jam’iyyar a zaben.
Gwamna Ganduje ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman ‘yan jam’iyyar APC da su hada kai da dan takarar shugaban kasa da abokin takararsa domin ganin ta samu nasara a zaɓen shekarar 2023.