Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya shawarci Bola Tinubu, mai rike da tutar takara a jam’iyyar APC da ya tafi ya kula da lafiyarsa maimakon neman kujerar shugaban ƙasa.

Da yake magana a yayin wata hira da AriseTV a ranar Lahadi, Kwankwaso ya ce yakin neman zabe yana da tattare da kalubale kuma Tinubu yana bukatar sassautawa saboda lafiyarsa.
Akwai batutuwa na nuna damuwa game da lafiyar Tinubu tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban Najeriya na gaba.

A watan Agustan shekarar 2021, an yi rade-radin cewa dan takarar na shugaban kasa a jam’iyyar APC na cikin wani mawuyacin hali na rashin lafiya.

Daga baya gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya musanta hakan inda ya ce Bola Tinubu na da lafiya kuma yana da karfi da kuzari.
Batutuwa game da lafiyar dan takarar na jam’iyyar APC, bai hana shi zagayawa a fadin kasar nan domin neman shawarin shugabanni a matakai daban-daban ba kan takararsa ta shugaban kasa a shekarar 2023.