Daga Khadija Ahmad Tahir
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu nasarar cafke wani mai suna Yakubu Abdulmumin mai shekaru 28 wanda ya tsere daga gidan yarin kuje da ke birnin tarayya Abuja.
Rundunar ta cafke shine a Sango-Ota da ke cikin karamar hukumar Ado-Oda/Ota a Jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Abimbola Oyeymishine ya tabbatar da kama shi ta cikin wata sanarwa da fitar a yau Laraba.
Kakakin ya ce Abdulmumin ya an same shi ne da laifin hada baki gurin aikata kisa a Jihar Kogi.
Abimbola ya kara da cewa rundunar ta kama Yakubu ne a lokacin da su ka samu bayanai akan a kusa da Sango Ota.
SP Sale Dahiru shine DPO mai kula da yankin bayan samun rahoton ya aike da jami’an sa gurin da aka kama Yakubu Abuulmumin din.
Bayan kamashi ya bayyana yan sandan cewa ya tsere daga gidan gyaran halin ne a ranar da mayakan Boko haram su ka kai hari gidan yarin.
Sannan ya kara da cewa babbar kotun Jihar Kogi ce ta aike da shi gidan yarin bayan ya aikata laifin da ake tuhumar sa da shi.
Ya ce an mika Abdulmumin ne gidan yarin na Kuje a ranar Litinin din da ta gabata.
Abimbola ya ce kwamishinan ƴan sandan Jihar Lanre Bankole ya baiwa sashen binciken manyan laifuka na Jihar izinin mayar dashi gidan yarin.