Gwamantin jihar kano ta musanta zargin tsohon skataren gwamanti na cewa ana amfani da gidauniyar ganduje domin tailstawa kiristoci komawa musulmi a jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba shine ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Laraba.

Ya ce babu tilastawa a addini kamar yadda ƙungiyar Ganduje Fandation ba ta taba musuluntar da wani kirista ko bamaguke sai da radin kansa.

A yan kwanakin nan ne aka jiyo sakataren Babachir lawal yana cewa gwamantin kano tana tilsatawa kiristoci zama musulmai a jihar.

Babachir Lawal ya bayyana haka ne lakacin da yake nuna kin goyon bayan zabin jam’iyar APC ta yi na tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima a matsayin wanda zai yiwa Bola Tinubu mataimaki a zaɓen shekarar 2023.

Sai dai gwamantin Kano ta ce ba ta yin haka ba domin ya sabawa koyarwar addinin musulunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: