Shahararren dan wasan kwallon kafar kasar faransa Ousman Dambele ya sabunta kwantaragin watanni shida da kungiyar sa ta Barcelona.
A safiyar wannan ranar ta Alhamis kungiyar Barcelona ta bayyana sanya hannun na Dambele a shafinta na Twitter.
Ousman da ake rade radin zai bar Catalan a wannan Kakar bayan kwantaragin sa ya kare ya sanya sabon kwantaragin da kungiyarsa ta Barcelona a yau.
Tun bayan nada sabon mai horaswa Xabi Harnandes a farkon shekarar 2022 ake tunanin tafiyar dan wasan zaman sa ko rashin zaman sa Barcelona.
Sai dai kungiyoyi da dama sun nemi daukar dan wasan kamar Paris Germany yayin da ake ci gaba da cinikayyar yan wasa.
Dambele Wanda kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta siyo daga Brussia Dortmund akan makudan kudade.
Osman Dambele ya taka rawar gani sosai a kungiyar Barcelona bayan lashe kofuna da dama da kuma taimakawa kungiyar a fanni daban daban tun zuwan sa a shekarar 2017 Catalan.