Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an sojin Najeriya da su tunkari ‘yan ta’adda tare da shafe su daga doron kasa.

Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a sansanin sojoji na Jaji da ke jihar Kaduna a lokacin da yake jawabi ga jami’an soji a wajen bikin yaye dalibai 247 na babban kwas na 44 na kwalejin soji da rundunar soji (AFCSC).

Ya ce shekaru 12 da suka gabata sun kasance kalubale ga Najeriya, duba da irin matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar.

A cewar shugaban, yawancin kalubalen tsaro da ake fuskanta a duniya a yanzu duk sun hada ko ina da wanda ba na gwamnati ba a yankuna daban-daban da kuma sassan duniya, yankin yammacin Afirka da kuma nahiyar Afirka da muke ƙauna ba su tsira daga barazanar tsaron ba.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da goyon bayan da ake bukata domin ganin an samu nasarar da ake bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: