Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama wani mai suna Kamala Lawan Abubakar mai shekara 33 wanda ya tsere daga gidan yarin kuje na Birnin tarayya Abuja.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar SP Gambo Isah shine ya bayyana hakan ya ce an kamashi ne a wata maboya a Unguwar Sale da ke karamar hukumar Danmusa a Jihar.
Kakakin ya bayyana cewa sun kama kammala ne a lokacin da su ka gudanar da wani bincike a cikin karamar hukumar.
SP Gombe Isa ya kara da cewa bayan kamashi ya bayyana musu cewa an kai shi gidan yarin ne sakamakon kamashi da wani ganye wanda ake zargi na tabar wiwi ne.
Gambo Isa ya ce da zarar sun kammala bincike akan sa za su mikashi ga hukumomin gidan yarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: