Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagoncin gwamna Abdullahi Ganduje ta hana ‘yan Adaidaita sahu aiki bayan ƙarfe 10:00 na dare.

Sabuwar dokar na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar yau Litinin, ya ce dokar zata fara aiki ne ranar Alhamis 21 ga watan Yulin shekarar 2022.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnati ta cimma matsaya kan sanya dokar ne a ƙarshen taron tsaro na jihar Kano.

Yace sun ɗauki matakin ne a wani kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a dukkan sassan jihar Kano.

Malam Muhammad Garba ya roki masu Adaidaita sahu su bi dokar sau da ƙafa, inda ya ƙara da cewa jami’an tsaro za su bi lungu da saƙo domin su tabbatar ana bin dokar ba tare da jayayya ba.

Bayan sanya dokar masu Adaidaita sahu za su rika aikin su daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa ƙarfe 10:00 na dare a kowace rana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: