Kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta Najeriya (ANAP), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta shiga yi ko kuma su rufe bangaren sufurin jiragen sama tare da hada kai da malaman jami’a.

A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ANAP, Kwamared Abdulrasaq Saidu ya fitar, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kawo karshen yajin aikin ba tare da bata lokaci ba.

Ƙungiyar ta lura cewa ci gaba da zama a gida da daliban manyan makarantu ke yi na kara haifar da munanan dabi’u a kasar yayin da dalibai ke yin wasu abubuwa marasa kyau da ke iya lalata makomarsu.

Sannan ta yi barazanar cewa za ta shiga yajin aikin na hadin gwiwa ta hanyar rufe bangaren sufurin jiragen sama idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa na biyan bukatun ASUU ba.

Kungiyar ta lura cewa yajin aikin na sama da watanni hudu ya kawo cikas ga harkar ilimi, kuma hakan ya zama abin kunya a idon duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: