Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta na kokarin kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman makarantar Jami a wato ASUU a Najeriya su ke yi.

Bayanin hakan ya fito ne lakacin da aka yi taron koli karo na 81 wanda aka gudanar a Yola babban birnin jihar Adamawa.

Sakataren ilimi David Adejo shine ya bayyana Inda ya ce gwamnati na ƙoƙatin shawo kan kungiyar malaman makaranta na ASUU domin karta kara shiga wani yajin aikin a nan gaba.

David ya ce gwamnati bata bacci kan wannan dalilin sakamakon ɗaliban su na zaune ba sa zuwa makaranta.

An so aji ta bakin David akan kungiyar malaman makarantun kwalleji su ma da suke yajin aiki ya ce ba jimawa suma za su dawo bakin aiki.

Kungiyar malaman makaranta ASUU wadda ta shafe sama da watanni biyar domin ganin gwamnati ta biya musu bukatunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: