Daga Yahaya Bala Fagge

Gwamantin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa kungiyar malaman makarantun jami’a a kasar ASUU za ta koma aiki nan da makonni biyu masu zuwa.

Hakan ya fito ne daga bakin mai taimakawa sugaban kasa ta fanin yada labarai Malam Garba Shehu a jiya laraba.

Ya ce yajin aikin da ASUU ta ke yi tsawon watanni biyar babu karatu zai zo karshe nan sati biyu masu.
Sai dai Garba shehu ya ce batun da ake yadawa na cewa shugaban kasa Mahammadu Buhari ya bai wa Mininstan Ilimi lakoci da su daidaita alamarin tsakanin ASUU da gwamanati ba gaskiya bane.
kuma mutane su daina yada labaran da babu sahihancinsu.
Malam garba ya ce sun tattauna da mminstan kwadago chirs Ngige inda ya tabbata masa da cewa za a koma karatu nan da makonni biyu.
Ƙungiyar ASUU kungiyace wadda malaman makaratn jami a suka bude karkashin jami oin kasa Najerya kuma an kafa ta ne a shekarar 1965.
Sannnan ASUU ta na neman wasu hakkokin ta daga gwamnati farawa da biyanta albashi da kuma alawuus alawus.