Bayan hallaka manoma huɗu ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 70 a ƙauyuka daban-daban na ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Al’amarin kuma ya faru a tsakanin ranakun Lahadi zuwa Litinin.
Wani tsohon shugaban manoma mai suna Ɗanladi Idris ya bayyana cewar, an sace mutane 19 a ƙauyen Tsamaye yayin da aka tafi da mutane 11 a ƙauyen Mazau da Marina.

Sa waau yara bakwai ƴaƴan wani Alhaji Malam wadanda aka sace su a ƙauyen Katume sannan wasu mutane takwas da aka sace au a ƙauyukan Garki da Ƴaradua.

Haka zalika akwai wasu mutane 15 waɗanda aka sace su daga kauyen Unguwan Lalle sai wasu bakwai da aka tafi da su daga ƙauyen Dangawo.
A jihar Katsina kiwa mutane tara aka hallaka a tsakanin Faskari, Bakori da karamar hukumar Funtua.
A ranar Talata ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Ruwan Godiya a ƙaramar hukumar Faskari sannan su ka kashe mutane shida.
A ranar Talatan dai ƴan bindigan sun kai hari ƙauyukan Kadirawa, Tafoki tare da awon gaba da dabbobi masu yawa.
Sai wasu mutane biyu da aka kashe a Gandun Sarki da ke karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
Sai mutum guda da aka kashe a garin Funtua.
Ƴan sanda a jihar sun tabbatar da hallaka mutane shida tare da daƙile wani hari a jiya Laraba.
A jihar Taraba kuwa mutane Talatin aka hallaka a wani hari da ƴan bindiga su ka kai ranar Laraba.
Lamarin ya faru awanni kaɗan bayan da mahara su ka kai hari kan wasu sojoji na bataliya ta 93 a ƙaramar hukumar Takum ta jihar.
Har yanzu ana ci gaba da fuskantar hare-haren yan bindiga a sassa daban-daban na faɗin Najeriya.