Mutane 30 ne ake kyauta zaton sun rasa rayuwarsu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Zaria zuwa Kano ranar Alhamis.

Hadarin ya afku ne da misalin karfe 5:30 na yamma a kusa da Hawan Mai Mashi a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna.
Abdurahman Yakasai, mataimakin kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya mai kula da shiyyar Zariya, ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Ya ce hatsarin motar ya hada da motocin bas kirar Toyota mai daujar mutane 18 guda biyu da kuma Volkswagen Gulf, inda ya kara da cewa ya faru ne sakamakon gudun wuce sa a.

Kwamandan sashen ya ce hukumar ta kiyaye hadura FRSC har yanzu ba ta tantance adadin asarar da aka tafka ba.
Sai dai ya ce ana kokarin samun cikakkun bayanai na wadanda abin ya shafa.
A halin da ake ciki, wani ganau mai suna Suleiman Mohammed ya shaida wa manema labarai cewa, saboda tsananin wutar da ta kama motocin uku, da kyar mutane suka iya kubutar da wadanda abin ya shafa.