Rundunar “yan sanda ta kama wani yaro dan shekara 17 da laifin fasa wani gida kwana daya bayan fitowar sa daga gidan yari a Jihar Legas.

Yaron wanda ya shafe shekaru biyu a gidan yarin na kirikiri ana zargin sa ne da zamowa daya daga cikin ‘yan kungiyar Asiri.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar “yan sandan Jihar ta Legas Benjamin Hundeyin shine ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter.

Benjamin ya kara da cewa yaron bayan ya shiga gidan ya kwashewa mutanen gidan kayayyakinsu.

Yaron mai suna Small Bottle bayan sake kamashi za su ci gaba da bincike a kansa daga bisani kuma su turashi gaban kotu domin yi masa hukunci