
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen Jihar Katsina Jibril Ibrahim Zarewa ya bayyana cewa za su hada hannu kungiyoyi domin wayar wa da mutane kai kan rijistar zabe.
Alhaji Jibril ya bayyana hakan ne a ya yin wata ziyara da shugabannin wata ƙungiyar wayar da kan jama’a su ka kai masa ofishin sa a Jihar.

A yayin jawabinsa Alhaji Zarewa ya shaidawa kungyar irin ayyukan da hukumar ke yi wanda doka ta bayar da damar yin su.

Alhaji Jibril Zarewa ya nuna farin cikin sa dangane da ziyarar da kungiyar ta kai masa tare da basu tabbacin cewa za su hada hannu da kungiyar wajen wayar wa da mutane kai domin yin katin zabe.
Zarewa ya kara da cewa duk da lokaci ya kure a yanzu amma an yi akan gaba domin kungiyar itama za ta taimaka sosai.
A jawabin shugaban kungiyar Farfesa Abduaziz Ahmad Mashi ya bayyana cewa za su hada kai da hukumar ne domin su wayar wa da al’umma a Jihar kai domin yin katin zaɓe wanda zai ba su damar kaɗa ƙuri’a a zaɓen shekarar 2023.