Sarkin Kano mai murabus Malam Muhammad Sanusi II ya bayyana sayen kuri’u a matsayin barazana ga tsarin siyasar kasar Najeriya.

Muhammad Sanusi II ya yi jawabi ne a wajen wani taro na musamman da cibiyar dakin karatun Olusegun Obasanjo ta shirya.
Muhammad Sanusi II ya ce ya na ganin sayen kuri’a yana kawo babban cikas wajen zaben shugabanni.

Taron da aka gudanar ta yanar gizo an tattauna ne a kan abin da ya shafi kafofin sada zumunta na zamani da kuma sha’anin rashin tsaro da zabe a Najeriya.

A jawabin na sa, Sanusi II yake cewa sayen kuri’u da aka fito da shi a lokacin kada kuri’a, raina dokar zabe ne, sannan rashin sanin darajar akwatin zabe ne.
Khalifan na Darikar Tijjaniya a Najeriya ya nuna takaicinsa a game da yadda mutane suke nunawa Duniya takardar zabensu bayan sun kada kuri’arsu a sirri, wanda ya ce hakan sam bai dace ba.